Isa ga babban shafi

Shugaba Weah mai barin gado ya ce ba shi da niyyar sake takara a Liberia

Shugaban Liberia mai barin  gado, George Weah ya ce ba shi da niyyar sake tsayawa takarar shugabancin kasar, bayan da ya sha kashi a kokarinsa na neman wani wa’adin mulki, kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka ruwaito a Litinin.

George Weah, shugaban Liberia mai barin gado.
George Weah, shugaban Liberia mai barin gado. © AFP
Talla

Weah, mai shekaru 57, wanda tsohon zakaran kwallon kafar duniya ne ya lashe zaben shugabancin Liberia a shekarar 2017, amma ya fadi a kokarinsa na neman wani wa’adin shugabanci a watan Nuwamban shekarar 2023, inda abokin hamayarsa Joseph Boakai ya kada shi.

A ranar 22 na watan Janairun nan ne ake sa ran Boakai zai sha rantsuwar kama aiki.

A yayin da yake jawabi ga dimbim mambonbin majami’ar da yake zuwa a Monrovia, babban birnin kasar a ranar Lahadi, Weah ya ce shekarunsa sun yi nisa, saboda haka ba zai yi  takara a  zabe kasar mai zuwa ba, domin a lokacin zai kai shekaru 63 da haihuwa.

Weah ya gode wa al’ummar Liberia saboda damar da suka ba shin a zama shugaban kasarsu, inda ya nanata cewa ba zai sake takara ba.

Weah bai bayyana abin da zai yi bayan ya sauka daga shugabancin Liberia ba, amma ya ce zai yi aikin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a kasashen da ke fama da talauci a duniya.

Weah ya sha yabo sakamakon yadda ya amince da shan kaye a don tabbatar da mika mulki cikin ruwan sanyi a yankin yammacin Afrika, wanda juyin mulki ya wa katutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.