Isa ga babban shafi

Chadi ta fara biyan diyya ga iyalan wadanda aka kashe a mulkin Hissene Habre

Gwamnatin Chadi ta sanar da fara biyan iyalan sama da mutane dubu 10 aka kashe a zamanin tsohon shugaban mulkin kama-karya na kasar, kuma wanda aka yanke wa hukuncin aikata laifukan yaki, Hissene Habre diyyar dala miliyan 16 da dubu 500.

Tsoho Shugaban Chadi Hissene Habre
Tsoho Shugaban Chadi Hissene Habre REUTERS/Moumine Ngarmbassa
Talla

Shugaban Hukumar Kare Hakkin Bil'adama ta kasar, Jidda Umar ne ya bayyana hakan cikin wani jawabi da ya fitar a jiya Talata.

Ya ce iyalan wadanda suka kai dubu 10 da 800, kowannensu ya samu Sefa dubu 925, kwatankwacin dala 1,529.

Kudaden da Kotun Duniya ta ce bai kai kashi 10 cikin 100 na Sefa biliyan 82 da aka umarci a biya wadanda kisan gillar ta shafa ba.

Hussaini Habare wanda ya rasu a shekarar 2021, ya mulki kasar Chadi daga shekarar 1982 har zuwa lokacin da Idriss Deby Itno ya hambarar da shi a shekarar 1990.

A shekarar 2017 wata kotun Tarayyar Africa ta yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai bisa samunsa da laifukan yaki kan fararen hula, sannan ta umarci kasar Chadi ta biya wadanda lamari ya shafa diyyar Sefa biliyan 82 ta hanyar saida kadarorinsa tare da neman taimakon kudade.

Ana tunanin sama da mutane du 40 ne aka kashe a lokacin mulkinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.