Isa ga babban shafi

Sojojin Faransa za su ci gaba da zama a Chadi- Faransa

Jean-Marie Bockel wakilin Emmanuel Macron a Afrika ya bayyana cewa Faransa za ta ci gaba da girke dakarunta a Chadi a yayin da take ja da baya a wasu wurare a Afirka biyo bayan rikice-rikice da wasu gwamnatocin soji.

Dakarun Faransa a yankin Chadi
Dakarun Faransa a yankin Chadi © Aurelie Bazzara-Kibangula / AFP
Talla

 

Tasirin Faransa a kasashen yammacin Afirka da ta yi wa mulkin mallaka ya ragu yayin da shugabannin sojoji da ke yaki da 'yan tawaye a Mali, Burkina Faso da Nijar suka kori sojojinta tare da karfafa alaka da Rasha.

Kimanin sojojin Faransa 1,000 ne ke jibge a kasar Chadi, daya daga cikin kasashen da ke samun raguwar adadin sojojin Faransa a yankin wanda Janar Mahamat Idriss Deby Itno ke mulki tun shekara ta 2021.

"Tabbas za mu zauna" a Chadi, in ji Jean-Marie Bockel, wakilin Macron a Afirka da aka dorawa alhakin tattaunawa kan sabuwar siyasar Faransa ta fuskar sojojin ta a nahiyar.

Shugaba Emmanuel Macron da Mahamat Idriss Deby na Chadi
Shugaba Emmanuel Macron da Mahamat Idriss Deby na Chadi AFP - LUDOVIC MARIN

Macron ya bukaci tattaunawa da hukumomin Chadi kan "canji ta fuskar kasancewar dakarun Faransa ganin kalubalen tsaro da  yankin kef ama da shi, in ji Bockel bayan ganawa da Deby Itno a N'Djamena.

Bockel bayan nuna goyan bayan Faransa ya kuma sanar da shugaban rikon kweariyar Chadi Mahamat Idriss Deby Itno cewa kama hanayar mika mulki ga farrar hula,shine abinda ya dace.

Tsohon dan takara a zaben Chadi Yaya Dillo
Tsohon dan takara a zaben Chadi Yaya Dillo © AFP/Issouf Sanogo

Deby Itno zai tsaya takara a zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 6 ga watan Mayu, a wani lokaci da yan adawa suka soma bayyana damuwa tare da nuna shaku dangane da sahihancin wannan zabe.

 A cikin makon da ya gabata ne aka kashe babban abokin hamayyarsa kuma dan uwansa Yaya Dillo Djerou.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.