Isa ga babban shafi

Mahamat Deby ya sanar da shirin tsayawa takara a babban zaben kasar

Jagoran gwamnatin sojin Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno ya bayyana aniyarsa ta yin takara a zaben shugaban kasar mai zuwa, wanda aka tsara za a yi a ranar 6 ga wata Mayun wannan shekarar, kwanaki 3 kacal bayan da aka kashe babban abokin hamayyarsa a wani yanayi mai sarkakiya.

Jagoran gwamnatin sojin Chadi Mahamat Idriss Deby Itno.
Jagoran gwamnatin sojin Chadi Mahamat Idriss Deby Itno. © Denis Sassou Gueipeur / AFP
Talla

Deby Itno ya dare karagar mulkin Chadi ne a shekarar 2021, bayan mutuwar mahaifinsa Idriss Deby Itno a yayin da ya ke jagorantar yaki da ‘yan tawaye, bayan sama da shekaru 30 a kan mukamin shugaban kasar da ke yankin Sahel.

Mahamat Idriss Deby Itno, ya bayyana a wani jawabi da ya gabatar wa al’ummar kasar cewa zai yi takarar shugabancin kasar a karkashin gamayyar da gwamnati ta hada.

A shekarar 2021 ce aka nada Deby a matsayin jagoraan gwamnatin soji, kuma a lokacin ne ya yi alkawarin mika mulki ga farar hula a cikin watanni 18.

Amma Deby ya tsawaita wannan wa’adi da karin shekaru 2, kuma gwamnatinsa ta yi amfani da karfi fiye da kima wajen murkushe masu zanga-zangar adawa da matakin nasa a watan Oktoban shekarar 2022.

A ranar Talatar da ta gabata ce gwamnatin sojin Chadi ta sanar da cewa a ranar 6 ga watan Mayu za ta gudanar da babban zaben kasar.

Masu lura da al’amura na cewa Deby mai shekaru 39 yana da yakinin lashe zabe, duba da cewa an kashe babban abokin hamayyarsa, kuma dan uwansa, Yaya Dillo Djerou, kuma ga shi mahukunta sun murkushe sauran ‘yan adawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.