Isa ga babban shafi

Gambia na muhawara kan yiwuwar janye dokar haramcin yiwa Mata kaciya

Majalisar wakilan Gambia ta yi zama na musamman don tattaunawa kan shirin kawar da dokar haramcin yiwa mata kaciya da kasar ta fara amfani da ita tun daga shekarar 2015, batun da tuni ya ja hankalin kungiyoyin kare hakkin mata na kasa da kasa.

Har yanzu akwai miliyoyin mata da ke fuskantar wannan kaciya duk kuwa da kiraye-kiraye kan illar hakan ga lafiyar Mata.
Har yanzu akwai miliyoyin mata da ke fuskantar wannan kaciya duk kuwa da kiraye-kiraye kan illar hakan ga lafiyar Mata. © REUTERS/Siegfried Modola
Talla

Idan har Gambia ta yi mi’ara koma baya kan wannan doka mai cike da sarakakiya za ta zama kasa ta farko daga yammacin Afrika da ta haramta kaciyar amma ta dawo ta warware dokar.

Kafin muhawarar majalisar dai, tun farko malaman addini masu ra’ayin gargajiya ne suka fara matsin lamba ga mahukuntan na Gambia wajen ganin an dawo da halascin yiwa matan kaciya daga haihuwa, wadda tun farko kasar ta haramta a shekarar 2015 karkashin mulkin Yahya Jammeh.

Dadaddiyar al’adar ta kaciyar mata wadda wanzamai na gargajiya ko kuma jami’an lafiya kan yi amfani da reza ko kuma aska mai kaifi wajen yanke wani bangare ko kuma ilahirin tsokar da ke can cikin gaban mace, na ganin kakkausar suka daga kungiyoyin kare hakkin mata da ke kallon shi a matsayin take hakki.

Wasu al’adu a nahiyar Afrika sun yi amannar cewa salon kaciyar na kange mata daga aikata zinace-zinace sai dai a wasu lokutan kaciyar kan haddasa zubar jini da ke kaiwa ga asarar rayuka.

‘Yan majalisar na Gambia na shirin kada kuri’a kan wannan batu ne don sauya hukuncin da ake amfani da shi kusan shekaru 9 da ya haramta yiwa matakan kaciya, batun da masu fafutuka ke ganin cewa warware dokar ka iya shafar hatta sauran dokokin kare hakkin mata da suka kunshi na auren wuri da sauransu.

Gambia mai rinjayen musulmi da yawan al’ummar da bata haura miliyan 3 ba, babbar kungiyar addini ta kasar ta bayyana kaciyar ta Mata a matsayin guda cikin koyarwar addinin Islama, batun da ya ja hankalin ‘yan majalisar tare da bukatar muhawara kan lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.