Isa ga babban shafi

Wani sabon rikicin ƙabilanci ya hallaka mutane 42 a arewacin Chadi

Ma’aikatar tsaron cikin gida a Chadi ta tabbatar da mutuwar akalla mutane 42 a wani rikici da ya barke tsakanin wasu ƙabilu biyu masu faɗa da juna da ke yankin gabashin ƙasar.

Wani yanki a Chadi da ke kunshe da 'yan gudun hijirar da rikicin ƙabilanci ya raba da muhallansu.
Wani yanki a Chadi da ke kunshe da 'yan gudun hijirar da rikicin ƙabilanci ya raba da muhallansu. REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

Ma’aikatar tsaron cikin gidan ta Chadi ba ta bayyana sunayen ainahin ƙabilun da suka tsunduma a rikicin ba, haka zalika mahukuntan basu fayyace tsawon lokacin da aka dauka ana wannan takun saƙa ba.

Sai dai wasu majiyoyi sun bayyana cewa ƙabilun yankin biyu da suka kunshi mafiya rinjaye a harkokin Noma da kuma masu kiwo a gabashin kasar ta Chadi sun shafe tsawon lokaci suna tafka rikicin game da wasu filaye bayanda kowanne bangare ke ikirarin mallakarsa, lamarin da a lokuta da dama ke kaiwa ga rikicin tare da haddasa asarar rayuka.

Sanarwar da ma’aikatar tsaron ta Chadi ta fitar ta ce yanzu haka an kame mutane 175 daga dukkanin bangarorin da suka shiga rikicin a kauyen Tileguey na lardin Ouddai, kauyen da rikicin ya kai ga konewarsa kurmus bayan da mayaka masu rike da makamai suka rika cinna wuta.

Kakakin ma’aikar tsaron ta Chadi Mahamat Charfadine Margui ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa yanzu haka hankula sun kwanta a yankin kuma ana tattaunawa tsakanin bangarorin biyu don samar da maslaha.

Yankin kudanci da gabashin Chadi wanda galibi al’ummominsa ke rike da makamai ana yawan samun tashin hankali tsakanin Makiyaya da Manoma da ke kai wa ga asarar rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.