Isa ga babban shafi

Liberia za ta samar da kotun binciken laifukan yaki a kasar

Majalisar dattawar Liberia ta amince da samar da kotun binciken laifukan yaki, don yiwa wadanda aka ci zarafinsu a lokacin yakin babasar da kasar ta fuskanta har sau biyu adalci.

Majalisar dattawar Liberia ta amince da samar da kotun binciken laifukan yaki a kasar.
Majalisar dattawar Liberia ta amince da samar da kotun binciken laifukan yaki a kasar. © Carielle Doe / Reuters
Talla

Shugaban kasar Joseph Boakai ne ya mika wa majalisar kudirin hakan, inda a watan da ya gabata majalisar dokokin kasar ta amince da shi.

Haka nan a zaman majalisar dattawar kasar na jiya Talata, kudirin ya tsallake karatu na biyu, bayan da sanatoci 27 daga cikin 29 suka amince da shi, wanda a yanzu yake jiran amincewar shugaba Boakai.

Wannan mataki dai ya samu amincewar masu fafutuka da kungiyoyin fararen hula da ke ta kiraye-kirayen ganin an gudanar da binciken laifukan yaki da aka yi a kasar a shekarun 1989 da kuma 2003.

Kimanin mutane dubu dari 2 da 50 ne dai aka kashe a yakin basasan kasar, ciki kuwa har da kisan kirashi da fyade da sanya yara a cikin aikin soja.

Kwamitin sasanta wa na kasar ne ya bada shawarar samar da kotu ta musamman da  za ta tuhumi wadanda ake zargi da aikata laifukan yaki, sai dai babu wasu kwararan matakai da aka dauka sai da zuwan shugaba Boakai da aka zaba a shekarar data gabata.

Idan har in aka samar da kotun, za ta yi aiki ne bisa tsarin dokokin kasa da kasa da kuma samun goyon bayan manyan hukumomi na duniya ciki har da Majalisar Dinkin Duniya.

To sai dai wasu ‘yan kasar basa goyon bayan samar da kotun, wacce suke ganin tadoda tsohon rauni za ta yi da kuma rushe dokar afuwa da ta taimaka wajen kawo karshen yakin basasan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.