Isa ga babban shafi

Joseph Boakai na da burin hada kan al'ummar Liberia

Zababben shugaban kasar Liberia Joseph Boakai ya gabatar da jawabinsa ga al'ummar kasar a gaban manema labarai, a kalamansa na farko ya yabawa George Weah, shugaban kasar mai barin gado, wanda ya amince da shan kaye, kafin hukumar zabe ta bayyana sakamakon a hukumance.

Zababben shugaban kasar Liberia  Joseph Boakai,
Zababben shugaban kasar Liberia Joseph Boakai, REUTERS - CARIELLE DOE
Talla

Joseph Boakai ya yi jawabi ga dukan 'yan Liberiya, da cewa :"Dole ne mu taru don sake gina ƙasar."

 Zababben shugaban kasar ya ce yana son bunkasa yankunan karkara, musamman yankin kudu maso yamma.

Dan takara Joseph Nyuma Boakai na Jam'iyyar UP a lokacin zantawa da manema labarai
Dan takara Joseph Nyuma Boakai na Jam'iyyar UP a lokacin zantawa da manema labarai REUTERS/Thierry Gouegnon

Ya kuma yi alkawarin kawo goyon baya da ta dace ga al'amuran jama'a cikin gaskiya.

Zababben shugaban kasar ya yi alkawarin yin jagoranci a kan gaskiya .

Zababben shugaban kasart Joseph Boakai tare da  George Weah wanda ya fadi a zaben kasar Liberia .
Zababben shugaban kasart Joseph Boakai tare da George Weah wanda ya fadi a zaben kasar Liberia . AFP/File

Boakai ya ce ba za a sake amfani da Jiha a matsayin makamin tsinke ba daga wasu tsirarun mutane don cutar da mafi yawan al’umma.

Bugu da kari, Joseph Boakai ya yi alkawarin fara yin garambawul ga bangarorin tsaro da shari'a, wani abin lura shine zababben shugaban kasar a jiya Laraba ya fara aiki tare da George Weah.

Wata majiya na nuni cewa zai kafa wata tawaga da ke da alhakin jagorantar sauyi don tabbatar da ci gaba da gudanar da al'amuran yau da kullum, har zuwa lokacin da aka shirya rantsar da shi a ranar 24 ga Janairu, 2024.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.