Isa ga babban shafi

Haɗarin kwale-kwale ya kashe sama da mutane 60 a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Rahotanni daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na cewa akalla mutane sittin ne suka mutu wasu da dama suka ɓace sakamakon nutsewar wani kwale-kwalen a birnin Bangui.

Rahotanni daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na cewa akalla mutane sittin ne suka mutu wasu da dama suka bace sakamakon nutsewar wani kwale-kwalen a birnin Bangui.
Rahotanni daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na cewa akalla mutane sittin ne suka mutu wasu da dama suka bace sakamakon nutsewar wani kwale-kwalen a birnin Bangui. ISSOUF SANOGO/AFP
Talla

Mazuna ƙauyen da ke aikin ceto, sun ce mutane da dama sun jikkata tare da bacewar wasu da dama, sakamakon iftilan da jiya jumma’a a kogin M’poko da ke kudu maso yammacin babban birnin kasar Bangui.

Shaidu sun ce katafaren kwale-kwalen mai tsawon mita 20 da fadin mita 3, na dauke da mutane sama da 300 da suka hada da mata da kananan yara da ke kan hanyarsu ta zuwa jana'izar sarkin kauyen Mokola, wanda ya rasu makon  da ya gabata.

Rahotanni sun ce kwale-kwalen ya rabu gida biyu, mintuna kaɗan bayan ya tashi daidai lokacin da ya isa wani bangaren kogin mai zurfi.

A cewar shaidu, yawan kayan da aka loda na iya zama sanadin nutsewar kwale-kwalen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.