Isa ga babban shafi

Kenya ta karrama babban hafsan sojojin ƙasar da ya mutu a hatsarin jirgin sama

Ƙasar Kenya ta yi bukin soji da na addini wajen karrama babban hafsan sojojinta da ya mutu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a wannan makon.

Ƙasar Kenya ta yi bukin soji da na addini wajen karrama babban hafsan sojojinta da ya mutu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a wannan makon.20/04/24
Ƙasar Kenya ta yi bukin soji da na addini wajen karrama babban hafsan sojojinta da ya mutu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a wannan makon.20/04/24 © Willium Ruto Facebook
Talla

Shugaban kasar Kenya William Ruto, tare da mataimakin Rigathi Gachagua da kuma madugun 'yan adawa Raila Odinga, sun halarci bikin a dakin taro na Ulinzi da ke Nairobi babban birnin kasar, inda sojoji su ka yi harbi har sau 19 na girmamawa.

Da misalin ƙarfe 1 na ranar yau agogon GMT a shiga da akwatin gawar Francis Omondi Ogolla lullube da tutar kasar Kenya zuwa ɗakin taron tare da rakiyar algaitan sojoji, kafin a yi shiru na minti daya domin karrama shi.

Ƙasar Kenya ta yi bukin soji da na addini wajen karrama babban hafsan sojojinta da ya mutu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a wannan makon.20/04/24
Ƙasar Kenya ta yi bukin soji da na addini wajen karrama babban hafsan sojojinta da ya mutu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a wannan makon.20/04/24 © Willium Ruto Facebook

Ogolla, mai shekaru 61, da wasu jami’an soji tara sun mutu a ranar Alhamis, lokacin da jirginsu mai saukar ungulu ya fadi a wani yanki mai nisa a yammacin kasar, ƙasa da shekara ɗaya tun bayan da shugaban ƙasar ya masa a matsayin shugaban sojojin ƙasar.

Ƙasar Kenya ta yi bukin soji da na addini wajen karrama babban hafsan sojojinta da ya mutu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a wannan makon.20/04/24
Ƙasar Kenya ta yi bukin soji da na addini wajen karrama babban hafsan sojojinta da ya mutu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a wannan makon.20/04/24 © Willium Ruto Facebook

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.