Isa ga babban shafi

Kotu ta kama Bankin BNP da hannu a kisan kiyashin Sudan

Wani alkali a Amurka ya yanke hukuncin cewa dole ne bankin BNP Paribas ya fuskanci tuhuma gaban kotu game da zarginsa da hannu a kisan kiyashin Sudan tsakanin shekarar 1997 zuwa 2011.

Tambarin bankin BNP Paribas.
Tambarin bankin BNP Paribas. © AP - Jacques Brinon
Talla

Mai shari’ar ya tabbatar da cewa bankin na Faransa ya saukaka wa gwamnatin Sudan aika-aikatar da ta yi ta hanyar sahale masa ayyukan bankin wajen kaucewa takunkumin da Amurka ta kakaba mata.

Kawo yanzu Bank National de Paris yaki cewa uffan dangane da wannan hukuncin, sai dai a baya ya taɓa daidaitawa da Amurka don ya biya tara kan haramtacciyar kasuwanci da ya gudanar da hukumomin Sudan wanda ya saɓa ƙa’idar  takunkumin.

Hukuncin da alkalin ya yanke, bisa wasu kwararan hujjoji da ke alakanta kudaden da bankin ya bayar kai tsaye, aka yi amfani da su wajen take hakkin bil’adama, ya ba da damar ci gaba da shari'ar.

Hukuncin na neman biyan diyya da ba’a fayyace ba ga mazauna Amurka da suka tsere daga yankunan da suka yi fama da rikici kamar Sudan ta Kudu da Darfur ko kuma tsaunukan Nuba, dangane da laifukan da aka aikata.

Tun a shekarar 2016 aka shigar da ƙarar, wanda aka yi watsi da ita a 2018 amma wata kotun daukaka kara ta tarayya ta sake farfado da batun a shekarar 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.