Isa ga babban shafi

MDD ta ce a yi bincike kan mutuwar dan fafutukan Libya da ke tsare

Tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Libiya ta bukaci mahukuntan da ke rike da ikon gabashin kasar, su gudanar da bincike kan mutuwar Siraj Dughman, bayan mutuwarsa a inda ake tsare da shi tun a shekarar bara.

Sakatare Jnar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakatare Jnar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. REUTERS/Lisi Niesner
Talla

A wani sako da tawagar ta wallafa a shafinta na X, ta ce Siraj ya rasa ransa ne a inda ake tsare da shi a sansanin sojoji na Rajma, mai nisan kilomita 27 ta gabashin birnin Benghazi.

Tawagar ta ce abin takaici ne mutuwar dan fafutukar, don haka ta bukaci hukumomi su gudanar da binciken kwa-kwaf dangane da musabbabin mutuwar sa.

Ma’aikatar tsaron Benghazi a cikin wata sanarwar bidiyo da ta fitar dangane da mutuwar Dughman, ta ce ya fado ta kai daga kan wani bututun da ke saman tagar bandaki, a lokacin da yayi yunkurin tserewa a ranar Juma’a.

Tun a shekarar 2011 Libya ke cikin rikici, bayan da kungiyar tsaro ta NATO ta taimaka wajen hambarar da gwamnatin Muammar Gaddafi, inda a shekarar 2014 kasar ta rabu gida biyu ta hanyar samun gwamnatoci a yankin Gabashi da kuma Yammacinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.