Trump da mukarrabansa na fuskantar tuhumar yunkurin jirkita sakamakon zabe
Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump na fuskantar zarge-zarge da suka hada laifukan da suka shafe zabe bayan da aka shafe shekaru biyu ana gudanar da bincike a kan yunkurin da ya yi na karkata akalar sakamakon zaben da ya nuna cewa ya sha kashi a hannun dan takaran jam’iyyar Democrats, Joe Biden.
Wallafawa ranar:
i
Masu gabatar da kara a Atlanta sun zargi Trump da aikata manyan laifuka 13, abin da ya kara jefa shi cikin matsaloli a gaban kuliya, kuma ya saka burinsa na neman shugabancin kasar a karo na biyu cikin hatsari.
Wasu Karin mutane 118 suna fuskantar wadannan tuhume -tuhume a kan wannan bincike da ake gudanarwa, ciki har da lauyansa, Rudy Giulianni, wanda yake da hannu wajen matsa lamba a kan sakamakon zaben shekarar 2020, da kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Amurka, Mark Meadows.
Trump, tare da sauran wadanda ake zargi sun ki amincewa da cewa Trump ya fadi zabe, kuma da gangan suka rika shiga cikin kulla munakisar sauya sakamakon zaben ta inda zai nuna cewa shi Trump din ne ya ci zabe, kamar yadda takardar zargin ta bayyana.
Lauyoyin da aka ambaci sunayensu a kan wannan dambarwa sun ki cewa uffan, wasu daga cikinsu kuma ba a same su ba don yi wa manema labarai bayani.
Wannan batu da ya ke nema ya kai Trump ya baro dai ya samo asali ne daga zantawa ta wayar tarho da tssohon shugaban ya yi da shugaban hukumar zaben jihar Georgia, Brad Raffensperger, inda yake bukatar sa ya yi aringizon kuri’u da za su goge rashin nasarar da ya yi a jihar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu