Isa ga babban shafi

Trump ya musanta zarge-zarge 37 bayan gurfana gaban kotun Miami

Bayan bayyanarsa gaban kotun Miami tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya musanta dukkanin zarge-zarge 37 da ake masa na aikata ba dai dai ba lokacin barin mulkin kasar.

Donald Trump bayan fitowa daga kotun Miami a jiya talata 13 ga watan Yunin shekarar 2023.
Donald Trump bayan fitowa daga kotun Miami a jiya talata 13 ga watan Yunin shekarar 2023. AP - Chuck Burton
Talla

Donald Trump wanda lauyan da ke kare shi Todd Blanche ya yi magana a madadinsa yayin zaman kotun na jiya a Miami, ya bayyana cewa sai da tsohon shugaban ya ajje dukkanin bayanan sirrin da ake bukata gabanin mika mulki ga Joe Biden haka zalika babu wani bayanin karya da ya fitar kan zarge-zargen da ake masa.

Trump wanda shari’ar ta jiya ke zuwa sa’o’I kalilan gabanin bikin zagayowar ranar haihuwarsa ba tun yanzu ba, ya jima ya na musanta dukkanin zarge-zargen da ake masa yayinda ya nanata cewa ba zai ce uffan a zaman shari’ar ba ko da ya ke zai yi jawabi ga dandazon magoya bayansa a gidansa da ke bakin ruwa a jihar ta Florida.

Zaman shari’ar na jiya talata dai ya zo ne kwanaki 10 bayan tsohon shugaban ya gurfana gaban kotun Manhattan a New York kan zarginsa da biyan makuden kudi ga wata jarumar fina-finan batsa don ta boye abin da ya shiga tsakaninsu a lokacin da ya ke yakin neman zabensa na shekarar 2015.

Hankula dai sun tashi yayin zaman shari’ar na jiya wanda ya kai ga tsaurara matakan tsaro lura da yadda magoya bayan Trump suka yi fitar dango zuwa kotun Miami da ya bayyana jiya talata.

Bayan fitarsa daga Kotun Trump ya yi wani rubutu a manhajarsa ta Intanet mallakinsa mai suna ''Truth Social'' inda ya ce babban abin takaici ne yadda Amurka ke ganin koma baya a kowacce rana karkashin mulkin democrat.

Yanzu haka dai Trump ya ci gaba da yakin neman zabensa duk da zarge-zargen da ke kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.