Isa ga babban shafi

Trump zai gurfana gaban kotun Florida kan tuhumar boye bayanan sirri

Yau Talata tsohon shugaban Amurka Donald Trump ke bayyana gaban kotun birnin Florida don amsa tuhuma kan zargin da ake masa na sakaci da wasu bayanan sirri, lokacin barin kujerar mulki.

Tsohon shugaban na Amurka Donald Trump na kallon tuhumar a matsayin wata yarfen siyasa don hana shi tsayawa takara.
Tsohon shugaban na Amurka Donald Trump na kallon tuhumar a matsayin wata yarfen siyasa don hana shi tsayawa takara. AP - John Bazemore
Talla

Donald Trump mai shekaru 76 da misalin karfe 3 na yammacin yau agogon Amurka ne ake sa ran fara yi masa shari’ar inda zai bayyana gaban kotun ta Miami tare da Walt Nauta mai shekaru 40 guda cikin wadanda ake zargi da taimakon Trump wajen kwashe bayanan sirrin tare da kaiwa gidan maimakon barinsa a fadar White House.

A makon jiya ne aka gurfanar da Trump gaban kotu bisa zarginsa da aikata wasu laifuka 37 da suka kunshi sakaci da wasu bayanan sirri kan sha’anin tsaro sai fitar da kalaman sanarwar karya da kuma hadin baki wajen yiwa bangaren shari’a zagon kasa.

Tuni dai tsohon shugaban na Amurka Donald Trump ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake masa yana mai cewa tuhumar da ake masa ba komi bane face yarfen siyasa a kokarin hana shi tsayawa takara a zaben kasar na badi.

Sai dai lauyan Trump ya nanata cewa, tsohon shugaban ba zai ce uffan kan tuhume-tuhumen da ake masa ba, sai dai zai gabatar da jawabi bayan bayyanar tasa gaban kotu a yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.