Isa ga babban shafi

Tawagar Alkalan New York ta sahale gurfanar da Trump a gaban kotu

Wata tawagar alkalai a birnin New York na Amurka ta tuhumi tsohon shugaban kasar, Donald Trump da laifin biyan kudin toshiyar baki ga wata jarumar fina-finan batsa a yayin yakin neman zabensa na shekarar 2016 don kada ta tona abin da ta ce ya gudana a tsakaninsu, lamarin da ya sa zai kasance tsohon shugaban Amurka na farko da ya taba fuskantar tuhuma a kan aikata  laifi a gaban kotu. 

Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump.
Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump. REUTERS - JONATHAN ERNST
Talla

Tuhumar da ake wa tsohon shugaban kasar mai shekaru 76, wanda ya  musanta aikata ba dai dai ba a kan abin da ke da nasaba da biyan toshiyar bakin da aka ce ya yi gabanin zaben da ya kai shi ga zama shugaban Amurka a shekarar 2016 zai jirkita alkiblar zaben shugaban kasa mai zuwa, wanda Trump ke fatan sake darewa karagar mulki. 

Za ta kuma kasance tabo na har abada ga tsohon jagoran, wanda ya tsallake rijiya da baya a kan yunkurin tsige shi lokacin da ya ke shugaban kasar har sau biyu, kana ya caza kan masu gabatar da kara a game da kutsen ginin majalisun dokokin kasar da batun wasu kundaye na sirri, amma sai ga shi a kan biyan toshiyar baki ga jarumar fina-finan batsa Stormy Daniels, tsohon shugaban zai gurfana gaban kotu. 

Lauyar da ke kare Trump, Susan Necheles ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ta na sa ran a gurfanar da shi a ranar Talata mai zuwa. 

Ofishin babban alkalin gundumar Manhantta Alvin Bragg ya tabbatar da tuntubar lauyar Trump don shirya yadda zai mika wuya. 

Trump ya yi watsi da wannan tuhumar, wadda ya bayyyana a matsayin cin zarafi na siyasa, ya na mai cewa kaikayi zai koma kan mashekiya. 

Yaran gidan siyasarsa a bangaren jam’iyyar Republican sun caccaki abin da suka kira bi-ta-da-kullin siyasa, wanda aka kitsa da zummar wargaza aniyarsa ta yin takara a zaben 2024. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.