Isa ga babban shafi

Gaza haduwar tawagar alkalan New York ya tilasta dage tuhumar Trump

Batun tuhumar da ake yiwa tsohon shugaban Amurka Donald Trump a game da bai wa wata jarumar fina-finan batsa makudan kudade a matsayin toshiyar baki don kada ta tona abin da ta ce ya taba shiga tsakaninsu ya dauki sabon salo a jiya Laraba, bayan da tawagar alkalan birnin New York ta gaza zama kamar yadda aka yi tsammani, lamarin da ya tilasta dage yanke hukuncin zuwa mako mai zuwa. 

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump.
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump. AP - Sue Ogrocki
Talla

Tun bayan da tsohon shugaban na Amurka Donald Trump da kansa ya sanar da cewa ana shirin kama shi a wannan makon, lamarin da ya sanya rade-radin yiwuwar gurfanar da shi a gaban kotu.

A Larabar nan, wani babban jami’in tsaro da ba a bayyana sunansa ba ya shaidawa akasarin kafofin yada labaran Amurka cewa an daga zaman tsaida shawarar a gurfanar da tsohon shugaban ko akasin haka, lamarin da jaridar ‘The New York Times’ ta bayyana a matsayin basa-bam-ba. 

Tawagar alkalan wadda ta saba zama a ranakun Alhamis wata majiya da ke kusa da lamarin, wanda ya kawo labarin daga zaman ya ce zai yi wuya a yi wani zama a wannan makon, abin da ya sa ake tunanin zai iya kai wa makon gobe. 

Trump mai shekaru 76 zai kasance shugaban Amurka na farko, tsoho ko mai ci, wanda aka taba tuhuma da aikata laifi a gaban kuliya, idan har tawagar ta kada kuri’ar goyon bayan tuhumarsa. 

Ana tuhumar Trump da aikata laifuka da dama da suka hada da yin jayayya da kayen da ya sha a zaben shugaban kasa na 2020, da kuma ingiza magoya bayansa su yi kutse a ginin majalisun dokokin kasar. 

Wasu na ganin wannan matsalar da ya shiga ka iya zama karfen kafa ga kokarinsa na sake takarar shugaban kasa a  shekarar 2024.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.