Isa ga babban shafi

'Yan sanda na cikin shirin ko-ta- kwana kan yiwuwar kama Donald Trump

Jami’an tsaron Amurka na ci gaba da zama cikin shirin ko-ta-kwana a birnin New York, yayin da a gefe guda magoya bayan tsohon shugaban kasar Donald Trump suka datse hanyoyin da ke kaiwa gidan jagoran nasu.

'Yan sandan birnin New York da ke Amurka cikin shirin ko ta kwana.
'Yan sandan birnin New York da ke Amurka cikin shirin ko ta kwana. AP - Eduardo Munoz Alvarez
Talla

Tun a ranar Lahadin da ta gabata, Trump ya bukaci magoya bayan nasa da su gudanar da zanga-zanga domin dakile yunkurin da ya ce jami’an tsaro na yi na kama shi, bisa tuhumarsa da biyan wasu haramtattun kudade gabanin zaben shekarar 2016 da ya lashe.

Wasu kafafen yada labaran Amurka sun yi hasashen cewa akwai yiwuwar wata majalisar alkalai ta amince da hujjojin neman a gurfanar da Trump a gaban kotu a wannan Laraba, sai dai babu tabbas kan rahoton, la’akari da cewar wadanda lamarin ya shafa sun ki yin karin bayani.

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump.
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump. AP - Sue Ogrocki

Idan har aka shigar da kararsa gaban kotu, Donald Trump mai shekaru 76, zai iya zama tsohon shugaban Amurka, ko kuma mai ci na farko da za a tuhume shi da aikata wani laifi, matakin da ka iya yin tasiri kan shirinsa na sake tsayawa takara a zaben shugaban kasa da ke tafe a shekarar 2024.

A na ta bangaren dai wasu majiyoyi sun ce tuni rundunar ‘yan sandan birnin New York ta shirya kamen da ba’a taba ganin irinsa ba a Amurka, inda za a tasa keyar tsohon shugaban kasar Amurka zuwa kotu, kuma watakila ma buga masa ankwa a hannu.

Kafar yada labaran NBC ta ruwito cewar rundunar ‘yan sandan birnin New York ta NYPD ta baiwa dukkanin jami’anta umarnin tsukewa cikin kakinsu, su kuma zauna cikin shirin basu umarnin cika aikin kamen da  ake zaton za su yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.