Isa ga babban shafi

Donald Trump ya bayyana gaban kotun hukunta manyan laifuka ta Amurka

Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump ya musanta zarge-zargen laifuka 34 da ake tuhumar sa da aikatawa, bayan wani bincike da ya gano cewa ya bawa wata jarumar fina-finan batsa mai suna Stormy Daniels, toshiyar baki.

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump kenan, lokacin da yake shirin bayyana gaban kotun hukunta manyan laifuka ta Manhattanm.
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump kenan, lokacin da yake shirin bayyana gaban kotun hukunta manyan laifuka ta Manhattanm. AP - Corey Sipkin
Talla

Trump wanda ya mika kan sa ga kotun hukunta manyan laifuka ta Amurka da ke Manhattan, shine shugaban kasar na farko da ya fara fuskantar tuhuma da ta danganci aikata manyan laifuka.

Rahotanni sun ce, tsohon shugaban na Amurka,  ya bawa jarumar fina-finan batsar kudin toshiyar bakin ne a shekarar 2016.

Bayan bayyana gaban kotu, Mista Trump ya wallafa sakon da yake yi wa mahukuntan kasar izgilanci, yana mai cewa da alama suna kokarin tsare shi ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.