Isa ga babban shafi
Isra'ila

Mahukuntan Isra’ila sun tsaurara matakan tsaro a Masallacin Kudus

Yunkurin da wasu al’ummar birnin kudus suka yi na gudanar da wata zanga-zangar goyon bayan al’ummar kasar Masar, mahukuntan kasar Isra’ila sun dauki matakan tsaron haramtawa wasu shiga harabar masallacin Kudus a daidai lokacin gudanar da sallar Juma’a.Wani Jami’in ‘yan sanda Micky Rosenfeld, yace sun dauki matakin haramtawa mutanen da ke kasa da shekaru 50 ne wadanda ke dauke da katin shaidar zama dan kasar Isra’ila domin kaucewa faruwar zanga-zangar.An dai kiyasta cewa mutane 6,000 ne suka samu damar halartar Sallar Juma’a a masallacin na birnin Kudus. Wannan matakin kuma na gwamnatin kasar na zuwa ne saboda dumuwa ga Palasdinawa dake yankin gabacin birnin kudus. 

Masallacin Al-Aqsa na birnin kudus
Masallacin Al-Aqsa na birnin kudus
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.