Syria
An bukaci kungiyar Larabawa ficewa daga Syria
Majalisar da ke Ba kungiyar kasashen Larabawa shawara, ta bukaci kungiyar ta janye wakilan ta dake sa ido a Syria, saboda tashin hankalin da ake cigaba da samu. Kakakin Majalisar kungiyar, Salim al Diqbassi, ya bukaci Sakatare Janar na kungiyar, Nabil al Arabi, da ya gaggauata janye wakilansu masu aikin sa ido a cikin kasar, saboda yadda ake ci gaba da kashe fararen hula.
Wallafawa ranar:
Talla
Yanzu haka mutane 286 ne aka kashe tun fara ziyarar wakilan kasashen a ranar 23 ga watan Disemba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu