Isa ga babban shafi
Syria

Shugaban Syria Assad ya yi Jawabi kan tashin hankalin da kasar ke fuskanta

Shugaban Kasar Syria, Bashar al Assad, ya zargi kasashen Yammacin duniya da yunkurin jefa kasar cikin halin kakanikayi, yayin da ya ce shi bai bada umurnin kai hari kan fararen hula ba.

Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad
Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad REUTERS/SANA/Handout
Talla

Yayin da yake jawabi ga Yan kasar, shugaban ya ce kasashen Yankin Gulf da na Yammacin Duniya ba zasu ci gaba da kitsa karya dan yaudara kasahsen duniya ba.

Shugaban Assad ya ce, ganin sun kasa cimma biyan bukata, yanzu haka wadanan mutane sun zama masu kisan mummuke, dake samun goyan bayan kafofin yada labaran duniya, abinda ya fito da rawar da kasashen duniya ke takawa a rikicin kasar karara.

Assad ya soki rawar da kungiyar kasahsen Larabawa ke takawa a rikicin siyasar kasar, inda yake cewa, duk da shirinsu na aiki da kungiyar, ba zasu bari a dakushe Yancin cin gashin kansu ba.

Shugaban ya ce, tun a shekarar 1917 aka kafa Majalisar kasar Syria, saboda haka wa zai nuna musu demokradiya. Shugaban ya ce, ko da sunan wasa, shi bai bada umurnin harbi kan fararen hula ba.

A karshe sai ya kira zaben raba gardama a watan Maris mai zuwa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.