Isa ga babban shafi
Syria-Kasashen Larabawa

‘Yan adawar Syria sun ce kasashen Larabawa sun manta da su

‘Yan adawa a kasar Syria sun kira wata kazamar zanga-zanga a yau Juma’a domin ci gaba da la’antar gwamnatin Bashar Assad tare da bayyana kokensu ga kasashen Larabawa wadanda suka kammala taronsu a Bagadaza ba tare da daukar matakin kalubalantar shugaba Bashar Assad ba.

Shugaban Syria Bashar al-Assad  a lokacin da yake ganawa da dakarun shi a wata Ziyara da ya kai birnin Baba Amr kusa da birnin Homs
Shugaban Syria Bashar al-Assad a lokacin da yake ganawa da dakarun shi a wata Ziyara da ya kai birnin Baba Amr kusa da birnin Homs Reuters/路透社
Talla

A wata Sanarwa da ‘Yan adawar suka yada a shafin Juyin juya halin kasar Syria, sun ce al’ummar Musulmi da kasashen Larabawa sun manta da su tare da cewa yanzu sun dogara ne da Allah domin cim ma nasara.

A jiya Alhamis ne kasashen Larabwa suka gudanar da taro a kasar Iraqi, taron da kasashen Sunni suka kaurace wa.

Sai dai bayan kammala taron kasashen sun amince da kudirin sasantawa tsakanin ‘Yan adawa da gwamnatin Assad sabanin bukatar ‘Yan adawa masu neman kasashen su mara masu baya domin kawo karshen mulkin Bashar al Assad.

A sanarwar da ‘Yan adawar suka yada sun yi jinjina ga kasashen Saudiya da Qatar wadanda suka fito Fili suka bukaci taimakawa ‘Yan adawa da Makamai tare da neman Bashar Assad yin murabus.

Sai dai a taron kasashen Larabawa, Fira ministan Iraqi Nuri al-Maliki yace taimakawa wani bangare da makamai a Syria kan haifar da yaki a kasashen Larabawa.

Majalisar Dinkin Duniya tace sama da mutane 9,000 ne suka mutu a Syria tun fara zanga-zangar adawa da Shugaba Bashar al Assad.

Muhimman shawarwarin da Shugabannin kasashen larabawa suka amince, sun hada da amincewa da matsayin kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da bukatun da Kofi Annan ya gabatar na neman tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.