Adadin mutanen da su ka mutu a gobarar Pakistan ya haura 310
Hukumomin Kasar Pakistan sun ce adadin ma’aikatan kamfanin yin takalman da suka rasu sakamakon hadarin gobara, ya haura 310, abinda ya dada jefa shakku kan kare lafiyar ma’aikata.
Wallafawa ranar:
Shugaban jami’an kashe gobarar Lahore, Ehtesham Salim, ya ce masu kamfanin sun kulle daukacin kofofin shiga ma’aikatar ne, dan zargi sata da suka ce ana musu, abinda ya sa ma’aikatan suka kasa tsira daga gobarar.
Babban jami’in gwamnatin Karachi, Roshan Shaikh, ya ce adadin na iya karuwa.
A yanzu haka an shigar da kamfanin da jami’an gwamnati karar aikata kisa.
Har izuwa yanzu ba a ga inda masu kamfanin su ke kuma ‘Yan sanda na nan na nemansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu