Harin Bom ya kashe mutane 23 a Pakistan kafin Taron D8
Wani harin kunar bakin wake da aka kai ga mabiya akidar Shi’a ya kashe mutane 23 a Pakistan a dai dai lokacin da shugabannin kasashe Takwas ke shirin gudanar da taron bunkasa tattalin arzikinsu a birnin Islamabad.
Wallafawa ranar:
‘Yan sandan Pakistan sun ce an kai harin ne a Rawalpindi da ke kusa da babban birnin Pakistan inda Mabiya Shi’a ke shirin gudanar da bukin Ashura da Tasu’a a watan Muharram.
Kungiyar Taliban a Pakistan ta fito da dauki alhakin kai harin bayan tayar da wani Bom kusa da masallacin mabiya Shi’a a Karachi.
A yau ne dai shugabannin kasashe guda Takwas za su gudanar da Taron bunkasa tattalin arzikinsu da suka hada da Najeriya da Iran da Turkiya da Masar da Bangladash da Indonesia.
Sai dai Rahotanni sun ce akwai tsauraran matakan tsaro da Pakistan ta dauka saboda karbar bakuncin Taron a Islamabad
Shugaban Masar Muhammed Morsi yace zai kauracewa taron a Pakistan domin sa ido wajen ganin yarjejeniyar tsagaita wuta ta zauna tsakanin Hamas da Isra'ila.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu