Isa ga babban shafi
MDD-Pakistan

MDD ta saka sunan kungiyar Haqqani cikin ‘Yan Ta’adda

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya saka sunan Kungiyar Haqqani ta Pakistan cikin jerin sunayen ‘Yan Ta’adda saboda alakar kungiyar da Taliban. An zargi kungiyar da kai hare hare a Afghanistan tare da yin garkuwa da mutane.

lokacin da aka kai hari a ginin oshin jekadancin Amurka a Kabul wanda ake zargin kungiyar Haqqani.
lokacin da aka kai hari a ginin oshin jekadancin Amurka a Kabul wanda ake zargin kungiyar Haqqani. Reuters/Ahmad Masood
Talla

Haka kuma an saka sunan Babban Jami’in kungiyar Haqqani Abdul Rauf Zakir, cikin jerin sunayen ‘Yan ta’adda da aka saka wa Tukunkumin hana yawo da fataucin makamai da kuma rufe ajiyar shi ta bankuna.

Kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya ya zargi kungiyar Haqqani da kai hare hare a Afghanistan, hadi da kisan mutane 8 da aka yi a birnin Kabul shekarar 2008, da wani hari da aka kai a wata Otel wanda ya kashe mutane 11 a Kabul.

Haka kuma ana zargin kungiyar Haqqani da kai wani hari a watan Satumba shekarar 2011 a ofishin jekadancin Amurka a Kabul wanda ya kashe mutane 6.

An zargi kungiyar Haqqani da yin garkuwa da mutane tare da hada hannu da kungiyar Taliban da wasu kungiyayin ‘Yan tawaye a Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.