Isa ga babban shafi
Pakistan

'Yan bindiga sun sace sojoji 22 a Pakistan

A kalla ‘Yan Bindiga 200 ne suka yi wa wasu sansanonin Sojin kasar Pakistan kawanya tare da yin garkuwa da Sojoji 22.‘Yan Bindigan sun kuma kashe a kalla jami’an tsaro 2, yayin harin da suka kai.Maharan sun yi dirar Mikiya ne a Sansanonin Sojin dake a Peshawar, wani birnin da ke yankin Arewa maso yammacin kasar, da muggan makamai, kamar Bindigogi masu Jigidar Harsasi da Turmin harba Rokoki.An shafe fiye da sa’a daya ana bata kashi tsakanin ‘Yan Bindigar da Sojin da suka tarar a wurin. 

Wasu 'yan bindiga a kasar Pakistan
Wasu 'yan bindiga a kasar Pakistan REUTERS
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.