Isa ga babban shafi
Afghanistan

‘Yan kungiyar Taliban sun kashe ‘Yan sanda uku a Kabul

Wasu ‘yan kunar bakin wake daga kungiyar Taliban sun kai hari kan wani ofishin ‘Yan sanda dake birnin Kabul, inda suka kashe ‘Yan sanda uku a sanyin safiyar yau Litinin. Tuni dai kungiyar ta dauki alhakin kai harin, wanda yasa dakarun tsaro na NATO suka kwashe sa’oi suna arangama da ‘yan kunar bakin waken. 

Wani soji a lokacin da ake arangama da 'Yan kunar bakin wake a Kabul.
Wani soji a lokacin da ake arangama da 'Yan kunar bakin wake a Kabul. Reuters
Talla

Rahotannin na nuna cewa, akalla an kashe uku daga cikin biyar na ‘yan kungiyar, a yayin da biyu daga cikinsu suka boya a wani gini suna harbin mutane.

Daga baya kuma, an kashesu, kamar yadda rahotanni suka nuna.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.