Isa ga babban shafi
Masar

An rantsar da Adly Mansur a matsayin shugaban rikon kwarya a Masar

Bayan da Soji a kasar Masar suka sanar da tumbuke gwamnatin farar Hula ta kasar Masar, An rantsar da Alkalin Alkalai na kasar Adly Mansour a matsayin shugaban rikon kwarya na kasar  Masar

shugaban rikon kwarya, Alkalin Alkalai na kasar Masar
shugaban rikon kwarya, Alkalin Alkalai na kasar Masar
Talla

An rantsar da Adly Mansour a matsayin shugaban rikon kwarya na kasar Masar ne kwana daya bayan da Soji suka tumbuke gwamnatin Muhammad Morsi na jam’iyyar ‘yan Uwa Musulmi a kasar Masar.

"Na rantse zan tabbatar da ganin al’amurran kasar Masar sun gudana kamar yanda ya kamata, zan kuma mutunta Kundin tsarin mulkin kasa, na girmama Dokar kasa kazalika da tabbatar da ingantaccen tsaro ga al’ummar kasar” a cewar Mansur.

Yana kammala Rantsuwar ne jami’an kasar ta Masar suka jinjina masa cikin murna.

A kai tsaye ne aka watsa bukin rantsar da Alkalin Alkalan ta kafar watsa labarai ta Talabijin din kasar, a yayin da wani babban jami’in Sojin kasar ke shaidawa Kamfanin dillancin labarai na AFP cewar Mursi na can tsare a hannunsu a wani wurin da ba’a bayyana ba, tun jiya.

Tun a jiya ne kasashen Duniya keta fadin albarkacin Bakinsu, da suka hada da Amurka da Birtaniya da Faransa,  da Majalisar dunkin Duniya da ta nuna damuwa akan yanda Sojin suka dauki wannan mataki mai zafi kuma cikin gaggawa.

A bangaren Rasha, ta bukaci ‘yan Siyasar kasar Masar da su yi hattara kar murna ta koma ciki.

Kasar Jamus a fili ta bayyana tsige Morsi da Sojin suka yi a matsayin koma-baya a harkar Dimokradiyyar kasar Masar, amma ta yi kira da a hau Teburin sasantawa.

Alkalin Alkalai Adly Mansour ya kasance shugaban rikon kwarya na kasar Masar ne, kwanaki Hudu da rantsar da shi a matsayin da yake.

Yanzu haka dai Sojin sun sanar da dakatar da yin amfani da Kundin tsarin mulkin kasar, tare da bayyana cewar za’a shata ranar da za’a gudanar da sabon zabe.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.