Isa ga babban shafi
Saudiya

Kerry zai gana da Jami’an gwamnatin Saudiya

Yau Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, zai gana da jami’an gwamnatin Saudi Arabiya a wani yunkuri na rarrashin kasar, kan rashin jituwar da ta fito fili tsakanin su kan rikicin Syria da dangantaka da Iran. 

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry
Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry
Talla

Ita Saudi Arabia na na gaba gaba wajen ganin an kuada gwamnatin shugaba Bashar al Assad na syria, kana kuma ganin sabuwar dangantakar da Amurka ke shirin yi da Iran, na iya kaiwa ga barin Assad a mulki, wanda Saudiyan bata bukata.

Iran na daya daga cikin kasahsen da ke goyan bayan Assad, kuma basa ga maciji da Saudiya a siyasar duniya.

Ita kuwa Amurka a daya banagaren ta sha alwashin kyautata dangantaka tsakaninta da kawayenta na kasashen na yankin larabawa da rikicin juyin juya halin ‘yan shekaru ya addabesu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.