Isa ga babban shafi
Syria

Mutane sama da 162,000 suka mutu a Syria

Kungiyar kare hakkin Dan Adam da ke sa ido a rikicin Syria tace ce kimanin mutane 162,402 suka mutu tun lokacin da rikicin kasar ya barke a watan Maris a 2011, cikinsu kuma akwai fararen hula 53,988, hadi da Yara kanana 8,607.

Wata Yarinya karama tana kokarin tsira daga hare haren da Dakarun Gwamnatin Bashar al Assad suke kai wa ‘Yan tawaye a Aleppo
Wata Yarinya karama tana kokarin tsira daga hare haren da Dakarun Gwamnatin Bashar al Assad suke kai wa ‘Yan tawaye a Aleppo REUTERS/Hosam Katan
Talla

Alkalumman Kungiyar ta Birtaniya sun ce ‘Yan tawayen Syria kimanin 42,701 aka kashe a rikicin kasar hadi da Mayakan jihadi 13,500 da suka kunshi Mayakan Al Nusra da masu gwagwarmayar kafa daular Musulunci a Iraqi.

Dakarun Bashar al Assad kimanin 61,170 suka mutu. Akwai kuma Mayakan kungiyar Hezbollah ta Lebanon 438 da suka mutu wadanda ke marawa dakarun Gwamnatin Syria  baya.

Rikicin Syria ya samo asali ne daga zanga-zangar kin jinin gwamnatin Bashar al Assad inda al’amarin ya rikide zuwa yakin basasa.

Dubun dubatar mutanen Syria ne suka tsere daga kasar zuwa makwabtan kasashe saboda kazancewar rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.