Isa ga babban shafi
Iraqi

Iraqi: Mayakan sa-kai sun yi atisaye a Bagadaza

Dubban Mayakan sa-kai masu biyayya ga shugaban mabiya Shi’a Mogtada al-Sadr sun gudanar da atisaye a Bagadaza dauke da makamai a yau Assabar a wani shiri na shiga yaki da masu gwagwarmaya da suka karbe ikon wasu biranen arewacin kasar.

Atisayen Mayakan Sa-kai a Iraqi a birnin Bagadaza
Atisayen Mayakan Sa-kai a Iraqi a birnin Bagadaza REUTERS/Wissm al-Okili
Talla

Wannan na zuwa ne bayan Mayakan da ke gwagwarmayar sun karbe ikon yankin da ke kan iyaka da Iraqi da Syria da ake kira Al-Qaim bayan Mayakan Al Qaeda da al Nusra da ke yaki a Syria sun fice.

Wani Kanal din ‘Yan sandan Iraqi ya tabbatar da cewa yankunan da ke kusa da kan iyakar sun fada ikon ‘Yan gwagwarmayar masu bin akidar Sunni da ke son ganin bayan gwamnatin Shi’a a Iraqi.

Gungun mayaka guda uku ne suka hadu suke yaki a Iraqi.

Yanzu haka kuma akwai dubban fararen hula da suka mika wuya domin yakar masu gwagwarmayar.

Dubban mutane ne sanye da kakin Soja suka gudanar da atisaye dauke da muggan makamai a birnin Sadr da ke arewa da Bagadaza, suna ihu tare da yayata kalaman yabo ga tsoffin shugannin Shi’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.