Isa ga babban shafi
China-India

Nerandra na ganawa da Xi Jinping akan harkokin kasuwanci da diflomasiya

Shugaban kasar China Xi Jinping na karbar bakuncin Firaministan India Narendra Modi wanda ya kai ziyarar kwanaki uku a kasar, domin inganta huldar kasuwanci da diflomasiya tsakanin kasashen biyu masu karfin tattalin arziki a yankin Asiya.Mista Xi na ganawa ne da Modi a mahaifarsa da ke lardin Shaanxi.

Firiya Minista India Narendra Modi
Firiya Minista India Narendra Modi Reuters/Ian Langsdon/Pool
Talla

Shugaban China Xi jinping na ganawa ne da Nerendra Modi na India a mahaifarsa lardin Shaanxi. Kuma wannan ne karo na farko da shugaban ke ganawa da wani shugaba a mahaifarsa birnin Xian.

Modi ya kawo zoyarar kwanaki uku ne a China domin inganta huldar India da China.

A bara dai Modi ya karbi bakuncin Mista Xi na China ne mahaifarsa da ke Jihar Gujarat.

Manyan kasashen masu karfin tattalin arziki a duniya na kokarin farfado da huldarsu ne da ta gurugunce musamman game da rikicin kan iyaka Himalayan inda aka gwabza yaki a 1962.

Kuma batun rikicin kan iyaka na daga cikin manyan batutuwan shugabannin kasashen na China da India zasu tattauna kai.

Sannan Neredra Modi zai nemi goyon bayan China domin samun kujerar dindin a MDD.

Amma batun huldar kasuwanci da tattalin arziki ne babban batun da shugabannin zasu tattauna akai musamman bayan China ta karkatar da hankalinta zuwa Pakistan sabanin India.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.