Cinikin jiragen yaki zai inganta huldar India da Faransa
Yarjejeniyar cinikin jiragen yaki 36, da India ta kulla da Faransa za ta kara inganta huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasahen ke fafutukar farfado da tattalin arzikinsu
Firaministan India, Narendra Modi a ziyarsa ta farko da ya kai kasar Faransa, ya bayyana cewa, ya bukaci mallakan jiragen yakin faransa 36 ne, kirar Rafel Jet domin su maye guraben jiragen yakin India da suka tsufa.
A shekara ta 2012, kasashen na India da Faransa sun kulla yarjejeniyar cinikin jiragen yaki, to sai dai hakarsu ba ta cimma ruwa ba, yayin da masana ke ganin cewa sabuwar yarjejeniyar ta wannan karan za ta kawo karshen cece kuce game da yarjejeniyar farko.
A danyan bangaren kuwa, yarjejeniyar cinikin na zuwa ne, a dai dai lokacin da Modi ke kokarin janyo hankulan masu saka hannnayen jari a kasarsa daga nahiyar turai, yayin da kuma yake fafutukar farfado da martabar India a idan Turai dangane da harkar kasuwanci.
Shi dai Shugaban Faransa Francois Hollande ya bayyana cewa kasashen biyu za su ci gaba da hulda mai tasiri
.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu