Isa ga babban shafi
India

Turmutsu-tsu ya hallaka mutane 27 a India

Wani turmutsu-tsu da ya auku a dai-dai lokacin da daruruwan mutane ke kokarin gudanar da ayyukan bauta a kudanci India ya yi ajali mutane 27.Kuma tuni aka sanar da ware musu wasu kudadde domin baiwa iyalansu a matsayin diya.

Friministan India Narendra Modi
Friministan India Narendra Modi Reuters/路透社
Talla

Rahotannin sun ce hargitse ya auku ne a yankin Rajahmundry wanda bisa al'ada mutane ke zuwa gabar kogi Godavari da ke yankin a iyakokin  Andhra Pradesh da Telengana,domin gudanar da addo'o'i na musamman.

Rahotan ya kuma bayyana cewa lamarin ya auku ne sa’o’I kadan a fara gudanar da addu’o’I da ke samun hallatar duban mutane kasar.

Mai magana da yawun Hukumomin yankin da lamarin ya auku Chandrababu Naidu ya tabbatar da cewa ba ya ga mutane 27 da aka tabbatar da mutuwar su, akwai wasu 29 da suka samu munannar raunika.

Tuni dai Firiya Minista Kasar Narendra Modi ya nuna takaicinsa da aukuwar lamarin, tare da mika ta’aziyar sa ga iyalan mamatan.

Wannan dai ba shine karon farko, da ake samun asara rayuka a lokacin bauta gabar kogi a India ba, sakamakon cikar kwari da rige-rigen shiga ruwan da suke yi domin gudanar da bautansu a bisa al'ada.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.