Isa ga babban shafi
Saudi-Arabia

Saudiya ta Cafke mayakan jihadi sama da 400

Hukumomin kasar saudiya sun sanar da karya lagwan wata babbar kungiya dake da alaka da mayakan jihadi na ISIS tare da cafke mambobiin kungiyar 431.

Masallacin Imam Ali ibn abi Talib da wani Dan kunar bakin wake ya kai hari a garin al Qadeeh a lardin Gatif na kasar Saudiya
Masallacin Imam Ali ibn abi Talib da wani Dan kunar bakin wake ya kai hari a garin al Qadeeh a lardin Gatif na kasar Saudiya REUTERS
Talla

Akasarin wadanda aka kama ‘yan asalin kasar ta sauydiya ne.

Ma’aikatar cikin gidan Saudiya ta bayyana cewa, tun a ‘yan makwannin da suka gabata ne, jami’an tsaro suka yi ta kokarin murkushe babbar kungiyar dake da kananan kungiyoyi a karkashinta.

A cewar ma’aikatar, kananan kungiyoyin nada hannu a hare haren ta’addaci da dama, da ya hada da harin kunar bakin wake da aka kaddamar a masallacin jumma’a na ‘yan Shia dake gabashin kasar ta saudiya yayin da kungiyar ISIS dake da’awar kafa daular Islama a Iraki da Syria ta yi ikirarin kai harin da ya lakume rayuka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.