Isa ga babban shafi
Japan

Ana bikin cika shekaru 70 da juyayin harin Hiroshima a Japan

Dubban mutane ne suka taru a kasar Japan don juyayin harin bam din da Amurka ta jefa a Hiroshima shekaru 70 da suka wuce wanda ya kawo karshen yakin duniya na biyu.

Bikin cika shekaru 70 da juyayin harin Hiroshima a Japan
Bikin cika shekaru 70 da juyayin harin Hiroshima a Japan REUTERS/Toru Hanai
Talla

Da misalin karfe 8 da minti 15 agogon Japan aka buga karaurawar juyayin tunawa da jefa bam din wanda Amurka ta jefa shekaru 70 da suka gabata.

Harin ya hallaka dubban mutane nan take, kuma wasu da dama suka mutu daga bisani.

Yara kanana da dattijai da kuma wakilai daga kasashe 100 suka halarci bikin inda suka dinga aje firanni don tunawa da ‘yan uwa da danginsu a wuri na musamman da aka kebe domin tunawa da wadanda bala’in ya ritsa da su a Hiroshima.

Firaminista Shinzo Abe da Jakadiyar Amurka Caroline Kennedy da kuma mataimakin Sakataren da ke kula da hana yaduwar makamai Rose Gottemoeller na daga cikin manyan jami’an Amurka da a karon farko suka halarci bikin.

Abe yace a matsayinsu na farko a duniya da aka kai wa hari da irin wannan makami, za su cigaba da yaki da yaduwar makamin nukiliya a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.