Sama da mutane 240,000 suka mutu a rikicin Syria
Kungiyar dake sa ido a rikicin kasar Syria tace mutane sama da 240,0000 aka kashe da suka hada da yara kanana 12,000 tun barkewar rikicin kasar a watan Maris din 2011.
Wallafawa ranar:
Kungiyar tace ta tattara adadin mutanen da suka mutu da suka kai 240,381, fiye da dadin da ta bayyana a ranar 9 ga watan Yuni.
Alkalumman kuma sun ce adadin yara kanana 11,964 aka kashe a Syria da fararen hula 71,781.
Rahoton kungiyar kuma ya ce an kashe Sojojin gwamnatin Syria kimanin 88,616 da suka hada da mayakan da taimaka ma su.
Sannan rahoton ya ce kimanin mutane 30,000 suka bata kuma babu wani bayani kan halin da suke ciki ko kuma inda suke.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu