Isa ga babban shafi
Indonesia

An fadada binciken jirgin Indonesia da ya bata

Masu aikin agaji sun fadada bincike zuwa gabashin kasar Indonesia domin nasarar samun wani da rai daga cikin mutane 54 da jirgin saman kasar ya fadi da su a karshen mako.

Lardin Papúa inda ake hasashen Jirgin Trigana Air na Indonesia ya bata
Lardin Papúa inda ake hasashen Jirgin Trigana Air na Indonesia ya bata Wikipedia commons/Alfindra Primaldhi
Talla

Rahotanni sun ce jirgin ya bata ne ranar Lahadi da rana sakamakon gurbacewar yanayi bayan ya tashi daga Jayapura babban birnin lardin Papua.

An bayyana cewa Jirgin na dauke da kudin da ya kai Dala 470,000 da za a rabawa talakawa a kauyukan kasar.

Shugaban gidan wayan kasar Haryono yace cikin jirgin har da ma’aikatansa hudu da ke rakiyar kudin.

Ba a ji duriyar jirgin ba minti 10 kafin ya isa inda ya dosa.

Masu aikin bincike sun hangi wani abu a yankin ya turnuke da hayaki, wanda ake has ashen tarkacen jirgin ne da ya fadi, kuma tuni kauyawan yankin suka ce sun hangi tarkacen cikin tsaunika a ranar Lahadi.

Zuwa yanzu dai babu bayani akan ko akwai wanda ya rayu daga cikin mutanen da ke cikin jirgin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.