Isa ga babban shafi
Myanmar

Shugaban Myanmar ya taya jam'iyar Suu Kyi murna

Shugaban kasar Myanmar Thein Sein ya bi sahun shugaban rundunar sojin kasar wajen taya jam’iyar Aung San Suu Kyi murnar gagarumar nasarar da ta samu a zaben kasar da kuma alkawarin mika mulki cikin kwanciyar hankali.

Shugaban kasar Myanmar Thein Sein.
Shugaban kasar Myanmar Thein Sein. Wikimedia Commons
Talla

Sakamakon zaben da ake ci gaba da bayar wa ya nuna cewar jam’iyar NLD na shirin lashe sama da kashi 85 na kujerun majalisar kasa.

Kawo yanzu jam’iyar ta samu kujeru 256 wanda ke nuna cewar tana bukatar karin 70 dan samun gagarumar rinjaye.

Suu kyi ta yi kirar sasanta al’ummar kasar tare da shugaban sojin da kuma shugaban kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.