Jam’iyyar Suu Kyi na kan gaba a zaben Myanmar
Wani Jigo a Jam’iyyar da ke mulkin kasar Myanmar ya ce sun sha mummunan kaye a hannun jam’iyar adawa ta Aung San Suu Kyi yayin da ake ci gaba da tattara sakamkon zaben kasar.
Wallafawa ranar:
Sakamakon farko ya nuna cewar Jam’iyar Suu Kyi ta NLD ta lashe kujeru 49 daga cikin 54 da aka sanar, kuma jam’iyar na neman kashi 67 ne dan samun rinjaye a Majalisar.
Wani babban jami’in jam’iya mai mulki Kyi Win ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar sun fadi kasa warwas a zaben.
An ruwaito Suu Kyi na bayyana fatar samun rinjaye a zaben da aka gudanar a ranar Lahadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu