Isa ga babban shafi
Iraqi-Syria

Kurdawa na rusa gidajen larabawa a Iraki

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce mayakan sa-kai na Kurdawa, sun rusa dubban gidajen larabawa da ke zaune a yankunan da mayakan na Peshmerga ke mamaye da su a arewacin Iraqi.

Mayakan sa kan Kurdawa na Peshmerga a Iraqi
Mayakan sa kan Kurdawa na Peshmerga a Iraqi Reuters/路透社
Talla

Amnesty ta ce an rusa gidajen ne bayan da hare-haren dakarun kawance suka kwato yankin daga hannun mayakan IS tare da mika shi a hannun Kurdawa a karshen 2014 zuwa farko-farkon shekarar da ta gabata.

A cewar wata Jami’ar Amnesty Donatella Rovera, rusa wadanan gidaje da dukiyoyin al’umma ba shi da maraba da aikata laifukan Yaki.

Ko a watan Oktober bara Amnesty ta fitar da irin wannan rahoto kan Syria, inda ta zargin kurdawan da aikata irin wannan laifi na rusa gidajen fararran hula da gan-gan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.