Isa ga babban shafi
Amnesty

Ana cin zarafin Mata ‘yan gudun hijira- Amnesty

Kungiyar Amnesty International tace akasarin mata ‘yan gudun hirar da suka isa Turai daga Syria da Iraqi sun fuskanci cin zarafi daga masu safararsu zuwa jami’an tsaro da kuma wasu maza da suke gudun hijira tare.

'Yan gudun hijirar Syria da ke kokarin shiga Turai ta Teku
'Yan gudun hijirar Syria da ke kokarin shiga Turai ta Teku AFP/AFP/
Talla

Kungiyar ta ce ta yi hira da 40 daga cikin matan da suka isa Jamus da Norway ta cikin kasar Girka da kasashen Balkans wadanda suka tabbatar da haka.

Tirana Hassan, Daraktar kungiyar tace matan da suke tafiya da yara ko kuma wadanda ba su da abokan rakiya suka fi fuskantar matsalar, inda ta bukaci gwamnatocin Turai da su kare matan.

‘Yan kasashen Syria da Iraqi da dama ne ke ci gaba da kwarara zuwa kasashen Turai ta tekun Mediterranean

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.