Faransa ta bukaci a sa ido ga ‘Yan Syria
Kasar Faransa ta bukaci kungiyar kasashen Turai da ta dada sa ido ga fasfo na bugi da wasu ke amfani da shi a matsayin na kasar Syria, musamman a kasashen Girka da Italia bayan kazamin harin da aka kai birnin Paris.
Wallafawa ranar:
Ministan cikin gida Bernard Cazeneuve yac e binciken kwa-kwaf kan fasfo da baki ‘Yan gudun hijira da ‘yan ci-rani ke gabatar wa a iyakokin Turai na da matukar tasiri domin kare al’ummar nahiyar.
Minsitan ya ce an sace fasfo din jama’a da dama a Yankunan da mayakan IS suka mamaye kuma wasu na amfani da su domin shiga kasashen Nahiyar Turai.
Akwai fasfo din Syria da aka tsinta kusa da gawar daya daga cikin maharan da suka kai jerin hare hare a Paris a ranar 13 ga watan Nuwamba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu