Isa ga babban shafi
Syria

Valls ya bukaci kasashen Gulf su karbi ‘Yan Syria

Firaministan Faransa Manuel Valls ya yi kira ga manyan kasashen Larabawa su amince da dubban ‘Yan gudun hijira da ke gujewa yaki a Syria. A cewar shi kasashen Turai ba za su iya karbar dukkanin ‘Yan gudun hijirar ba.

Firaministan Faransa Manuel Valls
Firaministan Faransa Manuel Valls REUTERS/Charles Platiau
Talla

Sannan ya bukaci a shawo kan rikicin kasar a siyasance ko ta diflomasiya.

‘yan gudun Hijirar dai na tsallakawa ne zuwa kasashen da ke makwabtaka da Syria amma manyan kasashen larabawa irinsu Saudiya da daular larabawa da Qatar da Bahrain suna takaita karbar mutanben na Syria.

Miliyoyan ‘Yan Gudun Hijira ne kuma a yanzu ke ci gaba da kwarara zuwa Turai ta hanyar tekun Mediterranean.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.