Isa ga babban shafi
Turkiya

An hallaka mutane a harin kunar bakin wake a Turkiya

Wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a bakin wasu shaguna da ke tsakiyar Istanbul a yau Assabar, inda mutane 4 suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata.

A na zaman dari-dari a Turkiya
A na zaman dari-dari a Turkiya REUTERS/Tumay Berkin
Talla

Harin na wannan lokaci na zuwa ne mako guda bayan harin birnin Ankara da mayakan Kurdawa suka dau alhakin halaka mutane 35.

A cewar ministan lafiyar kasar Mehmet Muezzinoglu mutane 36 ne suka samu rauni, sai dai 7 daga cikinsu na hali mai tsananin, 12 kuma baki ne ‘yan kasashen ketare.

Harin na wannan lokaci shine na 6 irinsa daga watan Yuli daya gabata zuwa yanzu, a yankin Istikal Caddesi da ake da rukunni shagunan, kuma matane da dama ke zuwa Siyaya.

Tuni dai kasar Amurka ta yi allawadai da harin da kawo yanzu babu wanda ya dau alhakin kai shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.