Isa ga babban shafi
UN-Syria

Syria ta zama kasa mafi hatsari a duniya-WHO

Hukumar lafiya ta duniya ta ce Syria ce kasar da ta fi kowace hadari ga ma’aikatan kiwon lafiya a duniya baki daya, idan aka kwatanta da sauran kasashe masu fama da rikici da suka hada da Palasdinu, Yemen da dai sauransu.

Syria kasa mafi hatsari a duniya, inji Hukumar lafiya ta Majalisar dinkin duniya
Syria kasa mafi hatsari a duniya, inji Hukumar lafiya ta Majalisar dinkin duniya AFP PHOTO / DELIL SOULEIMAN
Talla

Rahoton da hukumar ta WHO ta fitar ya ce an kai wa jami’an kiwon lafiya da ke aiki a kasashen 19 da ke fama da rikici hare-hare fiye da sau 600 inda aka kashe mutane sama da dubu daya, kuma a Syria ne matsalar ta fi kamari a cewar rahoton.

A daya bangare kuwa sabon rahoto da kungiyar nan da ke sa ‘ido kan rikicin kasar ta Syria ta fiyar, ya ce sama da mutane dubu 280 ne suka rasa rayukansu a tsawon shekaru biyar da kasar ta share tana fama da yakin basasa.

Sabbin Alkallumar da Kungiyar dake zamanta a britaniya ta fitar sun nuna cewa, mutane dubu 282,283 rikicin syria ya lakume rayukansu, wanda cikinsu akwai farrarran hula dubu 81,436, da kanana yara dubu 14,040, sai mata dubu 9,106.

‘Yan tawayen da ba mayakan Jihadin ba, sunyi sanadi rayukan mutane dubu 48,568, yayin da Mayakan Jihadi suka kashe mutane 47,095 cikinsu hada baki ‘yan kasashen ketare.

Rahotan Kungiyar, ya kuma bayyana mutuwar mutane dubu 101,662, mayakan sa kai dake goyowa gwamnati baya, sai dakarun Sojin Syria dubu 56,609 da suka kwanta dama.

Sai wasu dubu 3,522 da ba a bayyana tantacce su ba.

Tun a shekarar 2011, kungiyar take amfani da na’urorinta wajen tattara bayanan wadanda yakin basasar kasar ke lakume rayukansu.

Wannan dai ya kasance karo na farko da kungiyar ke fitar da wanann rahotan, tun bayan cimma yarjejeniya wucin gadi na tsakaita wuta dake tangal-tangal tsakanin gwamnati da ‘yan tawaye a ranar 27 ga watan Fabairu.

A cewar hukumar yarjejeniyar ya taimaka wajen raguwar alkalluman mammata a Syria da ta tattara daga lokacin da aka cimma yarjejeniyar zuwa yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.