Isa ga babban shafi
Turkey

Mummunan Harin bam ya hallaka mutane 11 a Istanbul

An kama wasu mutane 4 da ake zargi da hannu a kitsa harin bam da ya hallaka mutane 11 yau talata a birnin Istanbul.

Yansanda sun kama wasu da ake zargi da kai harin bam a Istanbul.
Yansanda sun kama wasu da ake zargi da kai harin bam a Istanbul. REUTERS/Yagiz Karahan
Talla

Harin dai an kai shi kan motar dake dauke da yansandan kwantar da tarzoma a yankin Beyazit daf da wuraren yawon bude ido dake Istanbul babban birnin kasar.

Baya ga mutanegoma sha daya da suka mutu akwai wasu sama da talatin da suka sami rauni kamar yadda gwamnan yankin Vasip Sahin ya sanar.

Kawo yanzu dai babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin duk da cewa shugaban Kasar, Recep Tayyib Erdoghan da ya ziyarci wadanda suka sami rauni a asibiti, ya danganta harin da aikin Kungiyar Kurdawa ta PKK ganin a baya kungiyar ta sha kai hare hare makamancin hakan a birnin na Istanbul.

Shugaba Erdoghan dai ya ce zai ci gaba da yaki da ta’addanci ya kuma sha alwashin kama tare da hukunta wadanda suke da hannu a harin na yau talata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.