Isa ga babban shafi
Iraqi

Dakarun Iraqi sun karbe Fallujah baki daya

Dakarun Iraqi sun karbe wuri na karshe daga hannun mayakan IS a birnin Fallujah, abinda ya kawo karshen arangamar wata guda da nufin ‘yanto birnin baki daya.

Dakarun Iraqi sun karbe birnin Fallujah baki daya daga hannun mayakan IS
Dakarun Iraqi sun karbe birnin Fallujah baki daya daga hannun mayakan IS AHMAD AL-RUBAYE / AFP
Talla

Tun a ranar 17 ga wannan watan ne, Firaministan Iraqi Haidar Al-abadi ya sanar da samun nasar tun bayan karya lagwan mayakan na IS masu da'awar kafa daular musulunci.

A cewar Al-abadi, wannan nasarar na a matsayin abin farin ciki ga daukacin al’ummar Iraqi wadanda ya ce, ya dace su yi biki saboda samun ta.

Arangamar da aka yi tsakanin bangarorin biyu ta bai wa dubban fararen hula damar ficewa daga garin na Fallujah domin tsira da rayukansu, yayin da hakan ya kara haifar da kalubale ga kasar dangane da daukan nauyin mutanen da yakin kasar ya tagayyara.

Mai magana da yawun rundunar yaki da ta’addanci a Iraqi, Sabah Noman ya ce, cikin kasa da sa’oi biyu ne dakarun kasar suka karbe yankin Jolan da ke arewa maso yammacin Fallujah daga hannun Mayakan na IS, abinda ya kasance babban koma baya ga kungiyar wadda ta dauki tsawon lokaci tana cin karenta babu babbaka a birnin.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.