Isa ga babban shafi
Syria

IS da ‘Yan tawayen Syria sun aikata laifukan yaki

Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta zargi ‘Yan Tawayen Syria da mayakan ISIS da laifufukan yaki, inda ta zarge su da sace jama’a tare da azabtar da su da kuma kashewa.

IS na ci gaba da tayar da kayar baya a sassan Syria
IS na ci gaba da tayar da kayar baya a sassan Syria REUTERS/Mohanned Faisal
Talla

Kungiyar ta bayyana sunayen kungiyoyi 5 da ke yaki da gwamnatin Syria a Arewacin kasar da suka hada da Al Nusra Front da Ahrar al Sham da Nureddin Zink da Levant Front da kuma Division 16 a matsayin masu aikata laifuka.

Amnesty tace kungiyoyin sun tsare lauyoyi da ‘Yan Jaridu da yara kanana da suka soki abin da suke yi tare da azabatra da su.

Philip Luther, Daraktan kungiyar a Gabas ta Tsakiya yace fararen hular na zaman cikin fargaba saboda abin da kungiyoyin ke yi.

Rahoton ya yi nazari ne akan ayyukan ‘Yan tawayen tsakanin 2012 da 2016.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.